Yadda Man Utd ke kamfar cin kwallaye tun bayan rabuwa da Ferguson

Anthony Martial, Marouane Fellaini da Alexis Sanchez Hakkin mallakar hoto PA
Image caption A karon farko Manchester United ta kasa cin Crystal Palace a gida tun shekarar 1970

An fi sanin Manchester United da wasa mai kayatarwa a gasar Premier, inda ta yi kaka-gida zamanin kocinta Sir Alex Ferguson.

A tsawon shekaru 26 na zamanin Ferguson, an yi zaratan 'yan kwallo maciya raga, kamar Eric Cantona da Ruud van Nistelrooy da Cristiano Ronaldo wadanda tarihin Old Trafford ba zai taba manta wa da su ba.

Akwai kuma wani lokaci da ake kira Ferguson Time, inda ana dab da tashi wasa, sai ya yi kokarin yadda za a zira kwallo a raga domin tsirar da Red Devils da maki uku.

Amma wannan yanzu ya zama tarihi, inda karfin United ke ci gaba da raguwa a zirara kwallaye a raga tun ritayar Ferguson a shekarar 2013.

Magoya bayan Manchester United dai na cikin kishirwar ganin 'yan wasansu na kai hare-hare domin ta haka ake da zarafin kada kwallo a raga maimakon tsarin kare gida.

Canjaras da Crystal Palace a ranar Asabar, shi ne karo na 65 da Manchester United ta yi canjaras a wasannin Premier a kaka 26.

Kuma kashi 31 na canjaras din, sun faru ne bayan Ferguson ya tafi.

Kuma Manchester ta fi yin canjaras fiye da sauran manyan abokan hamayyarta guda shida a gasar Premier.

Yawan canjaras tsakanin manyan kulob guda shida a Premier daga kakar 2013-14
Manchester United 20
Chelsea 14
Liverpool 14
Arsenal 12
Manchester City 12
Tottenham Hotspur 10

Sau uku United tana daukar koci bayan tafiyar Ferguson - David Moyes da Louis van Gaal yanzu kuma Jose Mourinho.

Babu mamaki idan Ferguson ya fi dukkaninsu yawan cin kwallaye.

Mourinho ya fi Van Gaal yawan cin kwallaye.

Yawan kwallayen Manchester United a Premier League
Koci Wasanni Kwallaye Yawan kwallaye a wasa
Sir Alex Ferguson 810 1,627 2.01
David Moyes 34 56 1.65
Jose Mourinho 89 142 1.60
Louis van Gaal 76 111 1.46

Dan wasan da ya burge a Manchester a kakar bana wajen cin kwallaye shi ne Anthony Martial, inda dan wasan na Faransa ya ci kwallo shida.

Amma babu wani dan wasa daga Manchester United da ke gogayya da sauran zaratan 'yan kwallo a kungiyoyin Premier.

Mohamed Salah da Harry Kane ne suka yi mamaya a kakar da ta gabata.

Salah ya karbi kyautar wanda ya fi zirara kwallo a raga inda ya ci 32 - tazarar kwallo biyu fiye da Kane.

A bana babu dan wasan Manchester United a sahun 'yan wasan da suka ci kwallo fiye da bakwai a raga.

'Yan wasan da suka fi cin kwallo a kakar 2018-19
Dan wasa Kwallaye Taimakawa a ci Yawan minti
Sergio Aguero 8 4 121
Pierre-Emerick Aubameyang 8 1 118
Raheem Sterling 7 6 134
Eden Hazard 7 4 125
Mohamed Salah 7 3 160
Harry Kane 7 1 166
Aleksandar Mitrovic 7 1 167
Glenn Murray 7 0 142