Wenger na son horar da Bayern Munich

Arsene Wenger Hakkin mallakar hoto Getty Images

Tsohon kocin Arsenal Arsene Wenger yana son karbar aikin horar da kungiyar Bayern Munich, wacce ke son Bafaranshen ya maye gurbin Niko Kovac, in ji Telegraph.

Tun da farko jaridar ta ruwaito cewa a farkon watan Nuwamba Wenger ya ki amincewa da tayin horar da 'yan wasan kungiyar Fulham.

Kocin ya nuna ba ya kaunar sake dawowa Ingila domin horar da wata kungiya bayan ya shafe shekara 22 a Arsenal.

Wenger ya ce yana fatan zai dawo aikin horar da 'yan wasa a farkon shekara, kuma jaridar Telegraph ta ce Bayern Munich yake hari.

Rahotanni daga Jamus sun ce tuni Wenger ya tattauna da Bayern Munich domin karbar aikin horar da kungiyar.

Tarihin Arsenal ba zai taba mantawa da Arsene Wenger ba, inda ya lashe kofin gasar Premier guda uku da kofin FA guda bakwai da Community Shield guda bakwai tsakanin 1996 zuwa 2018.

Labarai masu alaka