'Yan wasan Manchester United sun fi na Manchester City yawan albashi

Manchester United
Bayanan hoto,

Alexis Sanchez ya koma Manchester United a watan Janairu a kan fam miliyan 14 a shekara bayan haraji

'Yan wasan tawagar farko na Manchester United suna karbar kusan rabin miliyan na fam a shekara fiye da 'yan wasan Manchester City, a cewar wani sakamakon bincike kan yawan albashin 'yan wasa.

Kudaden da 'yan wasan Manchester United ke karba ya lunka kudin albashin da Tottenham ke biyan 'yan wasanta 11 na farko.

Barcelona ce kuma kungiya ta farko a bangaren wasanni da ke biyan matsakaicin albashi a shekara sama da fam miliyan 10.

Real Madrid da Juventus da kuma Manchester United na cikin jerin manyan kungiyoyi 10 da suka fi kashe kudi.

Sauran kungiyoyi guda shida daga cikin 10 na farko dukkaninsu sun fito ne daga kwallon kwando a Amurka.

Wadanda suka fi kashe kudi a Premier

Duk da Manchester City ta lashe kofin Premier a bara amma tana bayan Manchester United wajen biyan albashi, inda kulub din na Old Trafford ke kashe fiye da fam miliyan shida da rabi a shekara ga tawagar 'yan wasanta na farko.

City ce ta biyu inda take kashe fam 5,993,000, ga biyan albashin 'yan wasanta.

Chelsea ce ta uku da (fam 5,020,004), sai Liverpool ta hudu ( fam 4,862,963) sai Arsenal (fam 4,853,130) da kuma Tottenham (fam 3,515,778).