Abin da ya sa nake yi wa PDP aiki – Buba Galadima

Buba Galadima

Babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya PDP ta kaddamar da babban kwamitin yakin meman zabe na dan takarar shugabancin kasa Atiku Abubakar.

Sai dai baya ga jiga-jigan jam'iyyar ta PDP, kwamitin ya kunshi kusoshin wasu jam'iyyun hamayya, irin su Injiniya Buba Galadima wanda ke ikirarin shi ne shugaban gangariyar jam'iyyar APC, wato rAPC.

Ita dai rAPC wadda Buba Galadima ke wa jagoranci ta balle ne daga jam'iyyar APC mai mulkin kasar, lokacin da aka samu sabanin ra'ayi tsakanin 'ya'yanta.

Buba Galadima ya shaidawa wa BBC cewa yana cikin kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, wanda ake ganin fafatawa za ta fi zafi tsakaninsa da shugaba Muhammadu Buhari na APC.

Ya ce za su yi aiki tukuru wajen tabbatar da cewa an dawo da Najeriya bisa tafarkin da ya dace kamar yadda suka yi aiki tukuru wajen ganin APC ta kafa gwamnati a zaben da ya gabata.

Sai dai ya tabbatar da cewa rAPC din har yanzu tana nan a matsayin jam'iyya mai zaman kanta.

Galadima ya yi ikirarin cewa a halin yanzu Najeriya ba ta tafiya bisa tafarkin da ya dace. Ya ce "Najeriya ba ta tafiya daidai, tana tafiya a karkace, saboda haka dole mu gyara ta."

Ya kuma ce babu tantama PDP za ta kwace mulki daga hannun jam'iyyar APC.