Malcom ba zai yi wa Barcelona wasa ba

Malcom Barcelona Hakkin mallakar hoto Getty Images

Dan wasan Barcelona, Malcom zai yi jinyar mako biyu, bayan da ya yi rauni a kafarsa.

Barcelona ce ta sanar cewar Malcom zai yi jinyar kwana 10 zuwa 15, bayan da ya rauni a karawar da kungiyar ta doke Cultural Leonesa a Copa del Rey a ranar Laraba.

Hakan na nufin dan kwallon Brazil ba zai buga wa Barcelona wasan da za ta yi da Tottenham a gasar Zakaraun Turai ba.

Malcom ba zai kuma buga wa Barcelona karawar da za ta yi da Espanyol a gasar La Liga a ranar Asabar ba.

Tottenham za ta ziyarci Barcelona a ranar Talata a gasar cin kofin Zakarun Turai da burin yin nasara a Camp Nou, domin ta kai zagayen gaba a wasannin.

Labarai masu alaka