Nigeria: Ko kun san yawan kudin da Najeriya za ta lakume a 2019?

Buhari

Asalin hoton, Facebook/Nigeria Presidency

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kasafin kudin kasar da ya kai naira tiriliyan 8.91.

A watan Disambar 2018 ne dai Shugaba Buhari ya gabatar wa majalisar dokokin kasar kasafin na naira tiriliyan 8.83.

To sai dai majalisar ta kara naira biliyan 90 da miliyan 300 inda ta amince da kasafin na naira tiriliyan 8.91.

An tsara kasafin ne bisa hasashen Najeriya za ta fitar da gangar mai miliyan biyu da dubu dari uku a ko wace rana.

Har wa yau, an gina kasafin bisa hasashen farashin danyen mai kan dala $60 kan kowace ganga, da kuma kan farashin canji N305 kan dala daya.

Idan za a iya tunawa dai Shugaba Buhari ya sha tafi da ihu a majalisa, yayin da yake jawabi kafin gabatar da kasafin kudi na shekarar 2019.

Shugaban ya ce wannan shi ne jawabin gabatar da kasafin kudi na karshe a majalisar dokokin kasa ta takwas.

Wannan ne kuma kasafi na karshe da shugaban ya gabatar a wa'adin mulkinsa na farko da ke karewa ranar Laraba.

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto,

A jawabinsa, shugaba Buhari ya ce Najeriya ta fita daga koma-bayan tattalin arziki

A jawabin nasa, shugaba Buhari ya ce Najeriya ta fita daga koma-bayan tattalin arziki, sannan an samu raguwar hauhawan farashin kayayyaki, lamarin da ya janyo ma sa sowa da ihu daga bangaren 'yan adawa a zauren majalisar.

An ji wasu suna cewa "Karya ne," yayin da Buhari ke bayyana nasarorin gwamnatinsa.

Wasu 'yan majalisar kuma sun ta yi masa tafi domin karfafa masa guiwa.

Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta yi aiki da yawa duk da ba ta samu kudi da yawa ba, a fannin noma da ayyuka da lantarki da kuma raya al'umma.

Kuma ya ce a kowace jiha akwai aikin hanyoyi da gwamnatinsa ke yi.

Kuma ya ce gwamnatinsa ta yi kokari wajen taimaka wa jihohi da tallafi domin biyan albashi da kudaden 'yan fansho.

Sai dai ya ce a kasafin kudin na 2019, akwai triliyan 2.14 da aka ware domin biyan bashi.

Kasafin na badi ya zarce na bara inda shugaban ya ce gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali wajen kammala ayyukan hanyoyi da wasu na ci gaba da aka fara.

Jawabin Buhari a takaice

  • Najeriya ta fita daga matsalolin koma-bayan tattalin arziki
  • Hauhawan farashin kayayyaki ya ragu daga kashi 18.17 a Janairun 2017 zuwa kashi 11.28 a Nuwamban bana
  • Kudin ajiyarmu ya karu daga dala bilian $28.57 a Mayun 2015 zuwa dala biliyan $42.92 a tsakiyar Disemban 2018.
  • Mun yi kokari wajen magance matsalar tsaro a arewa maso gabas da rikicin kabilanci a wasu wurare
  • Mun samu nasara a yaki da cin hanci da rashawa
  • Mun hana shigo da shinkafa daga waje
  • Mun samu ci gaba sosai wajen ayyukan ci gaba
  • Mun yi kokarin kammala ayyukan da muka samu maimakon kirkirar wasu sabbi
  • A 2018 an yi aikin hanyoyi na nisan kilomita 1,531, an yi wa wasu kwaskwarima na nisan kilomita 1,008 a sassan Najeriya

Asalin hoton, Presidency

Bayanan hoto,

Wannan ne karon farko da aka yi wa shugaban Najeriya Ihu a majalisa

Yanzu haka kasafin kudin dai zai ya zama doka tun bayan da majalisa ta amince da shi.

Kasafin kudin shi ne na karshe a majalisar dokokin kasa ta takwas da za ta amince.