An kori dan jarida saboda rubuta labaran karya

Jaridar ta ce tana neman gano iyakar labaran karya da ya rubuta Hakkin mallakar hoto EPA

Mujallar Der Spiegel ta kasar Jamus ta kori wani dan jarida da ya sha lashe kyautukan yabo, bayan ta zarge shi da kirkirar maganganu da bayanai a cikin rahotanninsa.

Jaridar ta ce mutumin mai suna Claas Relotius ya rubuta labarai na karya tare kuma da kirkiro mutanen da babu su.

Mujallar ta ce wasu daga cikin wadannan labarai sun hada da wadanda suka samu yabo ko ma suka lashe kyaututtuka.

Dan jaridar, Mr Relotius, ya amsa cewa ya sharara karya a labarai kimanin 14 wadanda aka wallafa a jaridar ta Der Spiengel.

Cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, jaridar ta ce tana nan tana kokarin ganin ta gano iyakar karairayin da dan jaridar ya yi, bayan da wasu daga cikin abokan aikinsa suka nuna shakku kan irin rahotannin da yake kawowa.

Duk da cewa da farko ya musanta zarge-zargen, amma a makon da ya gabata, Relotius ya amsa laifin cewa ya sha kirkiro labarai, ko kuma wasu bayanai da yake cewa daga bakin wasu mutane ne, in ji jaridar.

A wasu labaran ma, an ce ya ce ya tattauna da wasu mutane, alhali bai taba haduwa da su ko tattaunawa da su ba, amma ya rinka kawo labari a kan su, ko ma rubuta wasu bayanai da yake cewa daga bakunansu ne.

Labarai masu alaka