Sanchez ya yi cacar za a kori Mourinho

Sanchez Mourinho

Asalin hoton, Getty Images

Dan wasan Manchester United, Alexis Sanchez ya musanta zargin da ake masa cewar ya yi caca da abokin kwallonsa cewar za a kori Jose Mourinho.

Wani rahoto da aka wallafa a ranar juma'a ya ce Sanchez yana bin Marcus Rojo fam 20,000 kudin cacar cewar United za ta sallami Mourinho daga aiki.

Sanchez wanda Mourinho ya dauko daga Arsenal a watan Janairu ya ce zargin da ake yi ba gaskiya bane.

Ya kara da cewar Jose ya ba shi damar murza-leda a daya daga kungiyar da ta yi fice a duniya, yana matukar godiya da damar da ya ba shi.

Kwallo hudu Sanchez ya ci wa United tun bayan da kungiyar ta doke Manchester City, yanzu kuma yana jinyar rauni.