Neymar ya je Brazil yin jinya

Neymar Brazil

Asalin hoton, Getty Images

Kocin Paris St Geramin, Thomas Tuchel ya tabbatar cewar sun bai wa Neymar izinin zuwa Brazil domin yin jinyar raunin da ya yi a lokacin gasar cin Kodin Zakarun Turai.

Neymar yana cikin 'yan wasan PSG da suka yi nasara a kan Red Star Belgrade da ci 4-1 a ranar 11 ga watan Disamba, kuma da shi aka kammala karawar.

Kocin na PSG ya ce Neymar ya karasa wasan da raunin a tare da shi, kuma sun amince ya je ya yi jinya a Brazil.

Hakan ne ya sa dan wasan bai buga karawar da kungiyar ta yi da Nantes a gasar cin kofin Faransa a ranar Asabar ba.