Har yanzu ba a doke Liverpool a Premier ba

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool ta doke Wolverhampton da ci 2-0 a wasan mako na 18 a gasar cin kofin Premier da suka fafata a ranar Juma'a.
Liverpool ta ci kwallo ta hannun Mohamed Salah a minti na 18 da fara tamaula, sannan mai tsaron baya Virgil van Dijk ya kara na biyu bayan da aka koma daga hutu.
Da wannan sakamakon har yanzu ba a doke Liverpool ba a gasar ta Premier, tana ta daya a kan teburi da maki 48.
Jumulla Liverpool ta buga wasa 18 a gasar shekarar nan, inda ta ci fafatawa 15 da canjaras uku, sannan ta ci kwallo 39 aka zura mata bakwai a raga.
Wasannin da za a buga a ranar Asabar:
- Arsenal da Burnley
- Chelsea da Leicester City
- Manchester City da Crystal Palace
- Newcastle United da Fulham
- West Ham United da Watford
- Huddersfield Town da Southampton
- Bournemouth da Brighton & Hove Albion
- Cardiff City da Manchester United