'Aubameyang zai ci kwallo 30 a Premier'

Pierre-Emerick Aubameyang

Asalin hoton, Getty Images

Sokratis Papastathopoulos ya ce abokin buka tamaularsa a Arsenal, Pierre-Emerick Aubameyang zai ci kwallo 30 a gasar Premier kakar 2018/19.

Aubameyang dan wasan tawagar Gabon ya ci kwallo biyu a 3-1 da Arsenal ta doke Burnley a gasar Premier wasan mako na 18 a ranar Asabar a Emirates.

Hakan ne ya sa dan wasan mai shekara 29 ya yi kan-kan-kan da Mohamed Salah na Liverpool, inda kowannensu ya ci 12 a raga.

Kawo yanzu Aubameyang ya ci wa Arsenal kwallo 22 a wasa 31 da ya buga mata Premier, tun komawarsa Emirates daga Borussia Dortmund.