'Yan Arsenal da dama na fama da jinya

Hector Balerin

Asalin hoton, Getty Images

'Yan wasan Arsenal da yawa na jinya a shirin da kungiyar ke yi na buga gasar Premier wasan mako na 19 da za ta ziyarci Brighton a ranar Laraba.

Wadan da ke jinya kuma ba za su buga karawar ranar Laraba ba, sun hada da Rob Holding da Konstantinos Mavropanos da kuma Hector Bellerin.

Ana sa ran likitocin Arsenal za su auna Nacho Monreal ko zai iya wasan, bayan da a wannan makon ne ake sa ran Shkodran Mustafi zai dawo atisaye.

Shi kuwa Henrikh Mkhitaryan zai yi jinyar sati shida, bayan da Danny Welbeck ke jinya mai tsawo.

Wasan mako na 19 da za a buga a Premier:

  • Fulham FC Wolverhampton Wanderers FC
  • Liverpool Newcastle United FC
  • Manchester United Huddersfield Town
  • Tottenham Hotspur Bournemouth FC
  • Leicester City Manchester City
  • Burnley FC Everton FC
  • Crystal Palace FC Cardiff City
  • Watford Chelsea FC
  • Southampton FC West Ham United