An yi hutun Kirsimeti a gasar La Liga

La Liga

Asalin hoton, Getty Images

Mahukuntan gasar cin kofin La Ligar Spaniya sun yi hutu, domin yin bikin shagul-gulan Kirsimeti da kuma na sabuwar shekarar da za ta kama ta 2019.

An kammala bugan wasannin mako na 17 a ranar 27 ga watan Disamba, inda aka yi fafatawa uku,

Barcelona ce ta daya a kan teburi da maki 37, sai Atletico Madrid ta biyu da maki 37, sai Sevilla ta uku da maki 32, sannan Real Madrid ta hudu mai maki 29.

Sai dai Real Madrid tana da kwantan wasa da za ta ziyarci Villareal a ranar 3 ga watan Janairun 2019.

Madrid ta buga gasar cin kofin Zakarun nahiyoyin duniya da aka yi a Abu Dhabi, kuma ita ce ta lashe wasannin.

Kwantan wasa a ranar Alhamis 3 ga watan Janairun 2019:

 • Villarreal da Real Madrid

Za a ci gaba da karawar mako na 19 a ranar 6 ga watan Janairun 2019 :

 • Deportivo Alaves da Valencia
 • Celta de Vigo da Athletic de Bilbao
 • Espanyol da Leganes
 • Real Madrid da Real Sociedad
 • Sevilla da Atletico Madrid
 • Real Valladolid da Rayo Vallecano
 • Getafe da FC Barcelona
 • Eibar da Villarreal
 • Levante da Girona
 • Huesca da Real Betis