Adikon Zamani: Batun Sadakin Aure Kashi na 2

Adikon Zamani: Batun Sadakin Aure Kashi na 2

Wannan ne kashi na biyu na shirin Adikon Zamani a kan batun sadakin aure wanda ke daga cikin abubuwan da kan janyo takardama tsakanin al'umma.

A matsayinsa na daya daga cikin ginshikan aure da Musulunci ya tanadar, muhimmancin sadaki ba ya misaltuwa.

Amma kamar yadda dukkan al'amarin dan Adam, an mayar da batun abu mai sarkakiya da wahalaswa har ya kai ga mutane ba sa iya gane ainihin dalilin da aka sanya shi tun da farko.

Daya daga cikin abubuwan da kan dami al'umma game da batun sadaki shi ne wani sabon salo da mazaje masu neman aure kan mika sadaki ga iyalan matar da za a aura tun kafin a daura auren.

Saboda wannan, sai kaga mutumin yana dora wa matar wasu bukatu wadanda na ma'aurata ne kawai, kuma wannan halayyar sai kara yawa ta ke yi.

Ta yaya lamarin ya kai ga wannan matakin? Yaya za mu iya dakatar da shi zama al'ada ta karfi da yaji?

A wanna makon mun tattauna da wasu mata da fitattun masana ilimin addinin Islama ne domin sanin ainihin yadda ya kamata a rika bayar da sadakin aure.