Liverpool ta kara ba da tazara a Firimiya

Liverpool

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Tazarar maki bakwai Liverpool ta ba Manchester City

Liverpool ta kara ba Manchester City tazara a teburin Premier bayan City ta sake shan kashi karo biyu a jere.

Maki shida yanzu Liverpool ta ba Tottenham da ta hauro matsayi na biyu wacce kuma ta lallasa Bournemouth 5-0.

Kwallaye 11 ke nan Tottenham ta ci a wasanni biyu a jere.

Liverpool ta caccasa NewcastleUnited ne 4-0 yayin da kuma City ta sha kashi 2-1 a gidan Leicester.

Lovren, da Salah da Shaqiri da Fabinho ne suka ci wa Liverpool kwallayenta a ragar Newcastle.

City yanzu ta dawo matsayi na uku a teburin firimiya tazarar maki bakwai tsakanin ta da Liverpool.

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United kuma ta doke Huddersfield 3-1 a Old Trafford.

Paul Pogba ya ci kwallaye biyu, kuma karon farko da ya ci kwallaye biyu a wasa daya tun karawarsu da Manchester City a kakar da ta gabata.

Wasa biyu a jere ke nan da Ole Gunnar Solskjaer ya yi nasara a Manchester United wanda ya karbi aikin rikon kwarya bayan korar Mourinho.

Ole ya bi sahun su Matt Busby da Dave Sexton da Jose Mourinho da suka yi nasara a wasanni biyunsu na farko a jere a matsayin kocin Manchester United.

Idan dai har Chelsea ta gaza doke Watford zai kasance maki biyar tsakaninta da Manchester United da ke matsayi na shida a tebur.

Wasu na ganin an fara ganin amfanin korar Jose Mourinho inda United ta sha yin barin maki a wasanni da dama.