Pep Guardiola ya gargadi Liverpool

Guardiola Kloop

Asalin hoton, Getty Images

Kocin Manchester City, Pep Guardiola ya gargadi Liverpool kan matsin da kungiya kan shiga idan tana kan teburin Premier.

A ranar Laraba a gasar Premier ne Liverpool ta ci gaba da zama ta daya a kan teburi, bayan da ta doke Newcastle United, Tottenham ta koma ta biyu ta dare matakin da City ke kai a baya.

Manchester City ta yi rashin nasara da ci 2-1 a hannun Leicester City, kuma hakan ya sa ta koma ta uku da tazarar maki bakwai tsakaninta da Liverpool.

Guardiola ya ce kungiyar da take ta daya a teburi kan fuskanci kalubale da dama ciki har da yadda kowa ke son doke ta, ga fatan da magoya bayanta kan yi na ta ci kowanne wasa.

Kocin ya kara da cewar idan kana son ka lashe kofin Premier kar ka yadda ka yi rashin nasarar wasanni da yawa.

Guardiola ya ce City za ta farfado daga koma bayan da ta ci karo da shi, za kuma ta koma kan ganiyarta.

City ta yi rashin nasara a wasa biyu a jere a bana, rabon da ta yi haka tun shekara biyu, kuam jumulla an ci ta karawa hudu a Premier shekarar nan.