Modric ya lashe kyautar gwarzon Balkan

Luka Modric

Asalin hoton, Getty Images

Dan wasan Real Madrid, Luka Modric ya lashe kyautar gwarzon dan wasan kudu maso yammacin Turai na shekarar 2018, wato Balkan Athlete of the year.

Modric dan kasar Croatia shi ne dan kwallon kafa na biyu da ya ci kyautar, bayan Hristo Stoichkov gwarzon dan kwallon kafar nahiyar Turai a shekarar 1994.

Dan wasan mai shekara 33 ya yi nasara ne da maki 77 a biki na 46 da kamfanin yada labarai na Bulgaria (BTA) kan gudanar, ya kuma doke Novak Djokovic wanda ya jera karo biyar yana lashe kyautar tun daga 2011 zuwa 2015.

Modric shi ne ya lashe kyautar Ballon d'Or ya kuma ci kofin Zakarun Turai da na Zakarun nahiyoyin duniya da Real Madrid, ya kuma kai Croatia wasan karshe a kofin duniya shi ne gwarzon gasar a Rasha.