'Liverpool za ta lashe Premier ba a doke ta ba'

Kloop Emery

Asalin hoton, Getty Images

Kocin Arsenal, Unai Emery ya ce Liverpool za ta bi sawun Gunners na lashe kofin Premier ba tare da an doke ta ba a kakar shekarar nan.

Arsenal za ta ziyarci Anfield a ranar Asabar a gasar Premier wasan mako na 20, Liverpool tana ta daya a kan teburin da tazarar maki shida, kuma har yanzu babu kungiyar da ta doke ta a bana.

Liverpool ta yi nasarar cin wasa takwas a jere tun 2-2 da ta yi da Arsenal a Emirates a ranar 3 ga watan Nuwamba.

Arsenal ce a cikin karnin nan ta lashe kofin Premier ba tare da an doke ta ba a kakar 2004, karkashin Arsene Wenger.

Emery ya ce yana ganin Liverpool za ta iya lashe Premier shekarar nan ba tare da an doke ta ba, domin tana da 'yan wasan da za su kai kungiyar ga yin nasara.