'Barcelona ba ta nemi sayen Rabiot ba'

Rabiot

Asalin hoton, Getty Images

Barcelona ta ce ba ta tattauna da dan kwallon Paris St-Germain, Adrien Rabiot kan batun daukarsa ba, amma tana son yin zawarcinsa.

Yarjejeniyar dan wasan za ta kare a karshen kakar bana a PSG, saboda haka zai iya tattaunawa da wasu kungiyoyin kan batun sayensa a watan Janairu.

Wasu rahotanni na cewar Barcelona ta yi magana da wakilan da suke kula da harkokin tamaular Rabiot din.

Hakan kuma laifi ne na karya ka'idar cinikin dan wasan tamaula, dalilin da kungiyar ta Spaniya ta musunta kenan.

Barcelona ta fitar da wani jawabi cewar ba ta aikata laifi ba, kan batun tuntubar dan wasan PSG.