Man City ta koma ta biyu a teburin Premier

Man City

Asalin hoton, Getty Images

Manchester City ta yi nasarar cin Southampton 3-1 a wasan mako na 20 a gasar cin kofin Premier da suka kara a ranar Lahadi.

Silva ne ya fara ci wa City kwallo a minti na 10 da fara wasa, daga baya Southampton ta farke ta hannun Højbjerg minti 27 tsakani.

City ta yi nasarar zura kwallo na biyu a raga bayan da mai tsaron bayan Southampton, Ward-Prowse ya ci gida, sannan daf da za a je hutu Aguero ya kara na uku a raga.

Da wannan sakamakon City ta hada maki 47 a wasa 20 a gasar ta Premier ta kuma koma ta biyu a kan teburi da tazarar maki bakwai tsakaninta da Liverpool ta daya.

Manchester City za ta karbi bakuncin Liverpool a ranar 3 ga watan Janairu a Ettihad a karawar mako na 21 a gasar ta Premier.