Solskjaer ya ci wasa uku a jere

Ole Gunnar Solskjaer

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United ta doke Bournemouth da ci 4-1 a wasan mako na 20 da suka kara a ranar Lahadi a Old Trafford.

United ta ci kwallayen ta hannun Pogba wanda ya zura biyu a raga da Rashford da kuma wadda Lukaku ya ci, ita kuwa Bournemouth ta zare daya ta hannun Ake.

Da wannan sakamakon United tana mataki na shida a kan teburi da maki 35 da tazarar maki uku tsakaninta da Arsenal ta biyar a kan teburin.

Kocin United na rikon kwarya Ole Gunnar Solskjaer ya ci wasa uku kenan a jere tun lokacin da ya fara jan ragama, ya kuma ci kwallo 12 aka ci shi uku.

Solskjaer mai shekara 45 ya yi kan-kan-kan da Sir Matt Busby da Jose Mourinho da suka ci wasa ukun farko da suka ja ragamar United.

A ranar Laraba ne United za ta fafata da Newcastle United a wasan mako na 21.