Kun san wasa nawa Madrid za ta yi a Janairun 2019?

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images

A ranar Talata ne za a shiga sabuwar shekarar 2019, inda a cikin watan farko na Janairun ne Real Madrid za ta buga wasa bakwai.

Real za ta fara da kwantan wasan mako na 17 da za ta ziyarci Villareal a gasar La Liga a ranar 3 ga watan Janairun 2019.

Daga nan ne za ta karbi bakuncin Real Sociedad a wasan mako na 18 a gasar La Liga da za su fafata a Santiago Bernabeu a ranar 6 ga watan Janairun.

Wasan Madrid na gaba shi ne wanda za ta karbi bakuncin Leganes a Copa del Rey wasan farko a ranar 9 ga watan a karawar kungiyoyi 16 da suka rage a wasannin.

A ranar 13 ga watan Janairu, Real za ta ziyarci Real Betis a gasar La Liga fafatawar mako na 19 daga nan a fada wasannin zagaye na biyu a gasar Spaniya.

Kwana uku tsakani Madrid za ta ziyarci Lagenes a wasa na biyu a Copa del Rey, sannan a ranar 19 ga watan Janairu, Real za ta karbi bakuncin Seville a wasan mako na 20 a La Liga.

Daga nan ne Madrid za ta yi wasa na bakwai a ranar 27 ga watan Janairu, inda za ta ziyarci Espanyol.

Real Madrid tana ta hudu a kan teburi da maki 29, Barcelona ce ta daya da maki 37, sai Atletico Madrid mai 34, sannan Seville ta uku mai maki 32.

Labarai masu alaka