Ronaldo ya kasa a shekarar 2018

Ronaldo Hakkin mallakar hoto Getty Images

Dan wasan tawagar kwallon kafa ta Portugal, Cristiano Ronaldo ya ce bai damu da rashin cin kofin gwarzon dan kwallon kafa a shekarar 2018 ba, bayan da ya lashe Ballon d'Or biyar.

Dan kwallon tawagar Juventus bai lashe kyautar hukumar kwallon kafa ta duniya da ta Turai UEFA ba, wadda dan wasan Real Madrid, Luka Modric ya karbe a 2018.

Ronaldo ya ce ya fi mayar da hankali kan nasarar kungiya, ba wai ta kashin kansa shi kadai ba, domin kwallon kafa ba ta mutun daya ba ce.

Haka kuma dan wasan na Portugal bai lashe kyautar dan wasan da ya taka rawa a gasar kofin duniya da aka yi a Rasha ba, ita ma Modric ne zakara.

Ronaldo ya lashe kofin Zakaraun Turai tare da Real Madrid, bayan da ta yi nasara a kan Liverpool da ci 3-1 a ranar 26 ga watan Mayun 2018.

Juventus tana ta daya a kan teburin Serie A, sannan ta kai zagaye na biyu a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League.

Haka kuma tawagar kwallon kafar Portugal ta kai wasan daf da karshe a Nations League, inda za ta fafata da Switzerland a cikin watan Yunin 2019.

Labarai masu alaka