Real Madrid ta dauki Brahim Diaz

Brahim Diaz Hakkin mallakar hoto Getty Images

Real Madrid ta kammala daukar Brahim Diaz daga kungiyar Manchester City kan yarjejeniyar sama da shekara shida.

A ranar Litinin Madrid ta sanar da daukar dan wasan mai shekara 19, bayan da likitocinta suka tabbatar da lafiyarsa.

Diaz mai buga tamaula daga tsakiya ya fara wasa a Malaga daga nan ya koma Manchester City da murza leda yana da shekara 16 a 2015.

Dan wasan tawagar Spaniya ya buga wa matasa 'yan 17 da 19, inda yanzu yake tare da 'yan shekara 21.

Real ta gabatar da shi gaban magoya bayanta, inda Diaz ya yi godiya da tarbar da aka yi masa, sannan ya buga kwallaye cikin 'yan kallo.

A karshen kakar bana ne yarjejeniyar Diaz za ta kare a Ettihad wadda ya buga wa wasa 15, sai dai bai yadda ya tsawaita kwantiragin da City ta gabatar masa ba.

Labarai masu alaka