FA Cup: Arsenal da Manchester United

Arsenal Man United Hakkin mallakar hoto Getty Images

Arsenal za ta karbi bakuncin Manchester United a wasan zagaye na hudu a gasar kofin kalubalen Ingila wato FA Cup.

Gunners ta lashe kofin FA sau 13, ita kuwa United tana da shi guda 12..

Mai rike da kofin Premier Manchester City za ta karbi bakuncin Burnley a Ettihad, yayin da Crystal Palace da Tottenham za su kece raini a Selhust Park.

Mai rike da FA Cup, Chelsea za ta fafata ne da wadda ta yi nasara tsakanin Sheffield Wednesday ko kuma Luton Town a stamford Bridge.

Yadda aka raba jadawalin

 • Swansea v Gillingham
 • Wimbledon v West Ham
 • Shrewsbury or Stoke v Wolves
 • Millwall v Everton
 • Brighton v West Brom
 • Bristol City v Bolton
 • Accrington v Derby or Southampton
 • Doncaster v Oldham
 • Chelsea v Sheffield Wednesday or Luton
 • Newcastle or Blackburn v Watford
 • Middlesbrough v Newport
 • Manchester City v Burnley
 • Barnet v Brentford

Labarai masu alaka