Salah ne gwarzon kwallon kafar Afirka na 2018

Mohamed Salah Hakkin mallakar hoto Getty Images

Dan wasan Liverpool, Mohamed Salah ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na 2018.

Dan wasan tawagar Masar ya yi nasara ne a kan Sadio Mane na Liverpool dan wasan tawagar Senegal da Pierre-Emerick Aubameyang na Gabon mai wasa a Arsenal.

An gudanar da bikin karrama 'yan wasan Afirka da suka yi fice ne a 2018 a fagen tamaula a Senegal.

Salah shi ne ya lashe kyautar 2017 da aka yi a Ghana.

Sauran wasu kyautukan da aka lashe:

  • Macen da babu kamarta: Chrestinah Thembi Kgatlana ta Afirka ta Kudu.
  • Matashin dan wasa: Achraf Hakimi mai taka leda a Borussia Dortmund dan kasar Morocco.
  • Kocin tawagar kwallon kafa ta maza: Herve Renard mai horar da Morocco.
  • Koci mace mai horar da tawagar mata : Desiree Ellis ta Afirka ta Kudu.
  • Tawagar kwallon kafa ta mata: Tawagar Nigeria ta Super Falcons.
  • Tawagar kwallon kafa ta maza: Tawagar Mauritania.

Labarai masu alaka