Golan Madrid Courtois zai yi jinya

Thibaut Courtois Hakkin mallakar hoto Getty Images

Real Madrid ta sanar cewar mai tsaron ragarta Thibaut Courtois zai yi jinyar kwana 10, ba zai buga Copa del Rey da Leganes a ranar Laraba ba.

Haka kuma golan ba zai buga gasar La Liga da Madrid za ta fafata da Real Betis da za su kece raini a Estadio Benito Villamarin ba.

Ana sa ran Courtois zai murmmurre kafin wasan La Liga da Real Madrid za ta yi da Sevilla.

Sauran 'yan kwallon Real da ke jinya sun hada da Gareth Bale da Toni Kroos da Javi Sanchez da kuma Mariano .

Labarai masu alaka