Watakila a bai wa Southgate kocin United

Gareth Southgate Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wasu rahotanni na cewa watakila Manchester United ta bai wa Gareth Southgate aikin horar da ita, domin maye gurbin Jose Mourinho da ta sallama a watan Disamba.

Ana ta rade-radin cewar Southagate mai horar da tawagar kwallon kafar Ingila, zai karbi akin kocin United a hannun Ole Gunnar Solskjaer, wanda ke jan ragama a rikon kwarya zuwa karshen kakar 2018/19.

Wasu na hangen cewar United za ta tuntubi Southgate wanda ya taka rawar gani a gasar kofin duniya a Rasha, ganin cewar da wuya Mauricio Pochettino ya bar Tottenham zuwa Old Trafford wanda ta ke son bai wa aikin.

Southgate mai shekara 48 ya kai tawagar Ingila wasan daf da karshe a gasar cin kofin duniya da aka yi a Rasha, sannan ya kai kasar wasan daf da karshe a wasannin Nations League.

Sauran wadanda ake alakantawa da aikin horas da United sun hada da Zinedine Zidane da kocin Juventus, Massimiliano Allegri.

Sai dai kuma kocin rikon kwarya Solskjaer na fatan a ba shi aikin na din-din-din, bayan da ya ci wasa biyar a jere da fara jan ragamar United din.

Labarai masu alaka