'Yan Madrid da ke jinya sun murmure

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images

'Yan wasan Real Madrid, Toni Kroos da Marcos Llorente da kuma Mariano Diaz sun halarci atisayen safiyar Talata tare da sauran 'yan kwallon kungiyar.

'Yan kwallon uku sun samu sauki bayan jinya da suka sha fama, ana sa ran watakila su buga wa Real Madrid Copa del Rey da za ta kara da Girona a ranar Alhamis.

Haka kuma matasan karamar Madrid, Cristo da kuma Javi Sanchez sun yi atisaye tare da manyan 'yan kwallon Real, sai dai Keylor Navas da Jesus Vallejo a jefen fili suka motsa jiki.

Shi kuwa Gareth Bale da kuma Marco Asensio sun yi ta wasa da tamaula ne a tsakaninsu a kokarin murmurewa da suke son yi daga raunin da suke jiya.

Labarai masu alaka