League Cup: Chelsea da Tottenham

Chelsea Tottenham Hakkin mallakar hoto Getty Images

Chelsea za ta karbi bakuncin Tottenham a wasa na biyu na daf da karshe a League Cup da za su fafata a ranar Alhamis a Stamford Bridge.

Tottenham ta yi nasarar doke Chelsea 1-0 a wasan farko na daf da karshe da suka fafata a ranar 8 ga watan Janairu a Wembley.

Kungiyoyin biyu sun kara a gasar League Cup sau tara, inda Chelsea ta yi nasara a fafatawa 4, Tottenham ta ci wasa uku da canjaras 2.

Tottenham ta yi nasarar doke Chelsea 3-1 a gasar cin kofin Premier bana da suka kara a ranar 24 ga watan Nuwamba a Wembley.

Tottenham tana ta uku a kan teburin Premier da maki 51, ita kuwa Chelsea tana ta hudu da maki 47.

Labarai masu alaka