Mario Balotelli ya koma Marseille

Mario Balotelli Hakkin mallakar hoto Getty Images

Mario Balotelli ya koma Marseille da taka-leda kan yarjejeniyar zuwa karshen kakar bana, bayan da ya bar Nice.

Dan wasan dan kasar Italiya ya so ya bar Nice tun kafin fara kakar bana, daga baya ya tsawaita zamansa, bayan da ya kasa samun wata kungiyar da zai koma buga tamaula a bara.

Balotelli mai shekara 28, bai ci kwallo ba a karawa 10 a kwanan nan, wanda Nice a ranar Laraba ta soke kwantiragin da ta kulla da shi.

Nice ce ta sanar da raba gari da ta yi da Balotelli a shafinta na Intanet, inda ta gode masa kan gudunmawar da ya bai wa kungiyar a kaka biyu da rabi da ya yi.

Tsohon dan wasan Inter Milan da Manchester City ya yi suna wajen zura kwallaye a raga a gasar Faransa, tun bayan da ya bar Liverpool zuwa Nice a 2016.

Balotelli ya ci kwallo 43 jumulla a zaman da ya yi a Nice, a bara guda 25 ya zura a raga a karawa 36 da ya yi, hakan ya sa tawagar kwallon kafar Italiya ta gayyace shi a watan Mayu.

Labarai masu alaka