Gombe United ta doke Kano Pillars

Gombe United Hakkin mallakar hoto NPFL

Gombe United ta yi nasarar cin Kano Pillars 2-0 a wasan mako na hudu a gasar cin kofin Firimiyar Nigeria da suka fafata a ranar Laraba.

Gombe ta fara cin kwallo ta hannun Usman Musa saura minti shida su je hutun rabin lokaci, bayan da suka sha ruwa suka koma fili ne Babangida Ibrahim ya kara na biyu.

Sakamakon wasannin mako na hudu:

  • Sunshine Stars 1-1 Rivers Utd
  • MFM 1-0 Rangers
  • Enyimba 0-0 Lobi
  • Insurance 0-0 Kwara Utd
  • Tornadoes 0-0 Remo Stars
  • FCIU 1-0 Yobe Stars
  • Heartland 1-0 Go Round
  • Akwa Utd 2-2 Plateau Utd
  • Abia Warriors 1-0 Kada City

Labarai masu alaka