Caraboa Cup: Chelsea ta ci Tottenham

Chelsea Tottenham Hakkin mallakar hoto AFP

Chelsea za ta kara da Manchester City a wasan karshe a gasar Caraboa Cup, bayan da ta yi nasara a kan Tottenham a bugun fenariti.

Chelsea ta yi nasarar cin Tottenham 2-1 a Stamford Bridge a wasa na biyu da suka kara a ranar Alhamis, inda a fafatawar farko Tottenham ta ci 1-0.

Hakan ne ya sa aka buga fenarity, inda Chelsea ta yi nasara da ci 4-2.

Man City ta kai wasan karshe ne bayan da ta doke Burton Albion 9-0 a Ettihad, sannan ta ci daya mai ban haushi a gidan Burton.

Da wannan sakamakon Chelsea ta kai wasan karshe za kuma ta fafata ne da Manchester City mai rike da kofin a ranar 24 ga watan Fabrairu.

Labarai masu alaka