Arsenal ta tuntubi Perisic na Inter Milan

Ivan Perisic Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ivan Perisic ya ci wa Inter Milan kwallo 34 a raga tun zuwansa a 2015

Arsenal ta tuntubi dan wasan Inter Milan Ivan Perisic.

Arsenal na son karbo dan wasan ne har zuwa karshen kaka, da nufin sayen shi kan fan miliyan 35.

A watan Satumba ne dan wasan ya sanya hannu kan sabuwar yarjejeniyar shekara biyar a Inter Milian har zuwa shekarar 2022.

Sai dai kuma yana da damar ya bar kungiyar da yake taka wa leda tun 2015 da ya zo daga Wolfsburg.

Perisic ya ci wa Inter kwallo 34 a raga a wasa 142, ya kuma ci kwallo uku rigis sau 25.

Dan wasan na Croatia mai shekara 29 ya taba taka leda a Borussia Dortmund da Club Brugge.

Arsenal dai na neman ta karbo dan wasan tsakiya da kuma dan wasan gaba inda take ci gaba da farautar dan wasan Barcelona Denis Suarez da Christopher Nkunku na Paris St-German.

Kuma Unai Emery yana neman ya kara wa tawagarsa karfi idan ya karbo Perisic.

Ana ganin Inter za ta amince da tayin fan miliyan 35 zuwa miliyan 40, duk da ta yi watsi da tayin da Manchester United ta yi a 2017 na fan miliyan 50.

Labarai masu alaka