FA Cup: Man City ta kai zagaye na biyar

Manchester City ta doke Burnley Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gabriel Jesus ya ci kwallaye takwas a wasa biyar

Manchester City ta tsallake zuwa zagaye na biyar a gasar FA bayan ta caccasa Burnley ci 5-0.

Gabriel Jesus da Bernardo Silva da Kevin de Bruyne da Sergio Aguero ne suka ci wa City kwallayen a ragar Burnley.

Pep Guardiola wanda ya lashe wa City kofin Premier da Carabao a bara, yana harin lashe kofi hudu a kakar bana.

Manchester City za ta hadu da Chelsea a wasan karshe na kofin Carabao, sannan za ta hadu da Schalke a zagaye na biyu a gasar zakarun Turai.

City da ke matsayi na biyu a teburin Premier, tazarar maki hudu ne ya raba ta da Liverpool da ke jan ragamar teburin, kuma ga shi yanzu ta kai zagaye na gaba a gasar FA.

City ta ci kwallaye 30 a wasanni bakwai da ta buga a 2019.

Labarai masu alaka