Da gaske Olivier Giroud zai bar Chelsea?

Giroud Hakkin mallakar hoto Getty Images

Dan wasan Chelsea kuma dan wasan gaban Faransa Olivier Giroud, mai shekara 32, ya bayyana cewa akwai yiyuwar ya koma gida ya ci gaba da taka leda. Wannan ya zo ne bayan da kungiyarsa ta dauko aron dan wasan Argentina, Ganzalo Higuain daga Juventus.

Dan wasan tsakiyar Faransa Adrien Rabiot ya ki amincewa da tayin Tottenham, inda dan shekara 23 ya ce ya son zuwa Liverpool.

Dan wasan gefe na Everton Yannick Bolasie ya shaida wa kungiyarsa cewa yana so a bayar da aronsa ga wata kungiyar a gasar Firimiya bayan da ya gajarta zamansa a kungiyar Aston Villa.

New Castle da Burnley da Cardiff na zawarcin dan wasan.

Har yanzu Arsenal na fatan cinmma yarjejeniyar sayen dan wasan Barcelona dan asalin kasar Brazil Malcom mai shekara 21, kafin zangon sayen 'yan wasa ya kare.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Paris St-German ta yi tayin Euro miliyan 21.5 domin sayen dan wasan Everton Idrissa Gueye dan asalin kasar Senegal. Amma Toffees ya bayyana cewa dan shekara 29 din ba na sayarwa ba ne.

Southampton ta yi tayin Fam miliyan takwas a kan dan wasan gaban Birmingham, Che Adams. Kungiyoyi 12 ke neman dan wasan mai shekara 22 wanda dan asalin Burtaniya ne.

Kungiyar Manchester City na ci gaba da tattaunawa a kan Hajduk Split mai shekara 18, inda ta yi tayin fam miliyan 5.5. ga dan wasan dan asalin kasar Croatia.

Dan wasan Leicester kuma dan asalin kasar Portugal mai buga tsakiya, Adiren Silva na son ya bar kungiyar kafin a kulle zangon sayen yan wasa.

Dan wasan mai shekara 29 bai samu buga wani wasa ba tun da kakar wasan bana ta fara.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kungiyar The Foxes na cikin tattaunawa da Monaco a kan dan wasan tsakiyar Belgium Youri Tielemans, mai shekara 21.

AC Milan na kan bakanta na sayen dan wasan Watford kuma dan asalin kasar Spain Gerard Deulofe mai shekara 24.

Kocin Stoke City Nathan Jones, na son yi ma kungiyarsa garanbawul, inda ake tattaunawa sayen yan wasansa uku, Bojan da Darren Flectcher da kuma Peter Crouch.

Martin O'neil na Nottingham Forest na bukatar dan wasan baya na West ham Reece Oxford mai shekara 20. Kungiyar mai buga gasar Championship na yunkurin yin tayin fam miliyan 8.

Oxford ya zauna a matsayin dan wasan aro a Bundesliga, inda Eitratch Frankfurt ke neman sayensa a wannan watan.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Liverpool Liverpool na tattaunawa domin sayen dan wasan Italiya mai shekara 18 Sandro Tonali daga Brescia.

Labarai masu alaka