Alvaro Morata ya koma Atletico Madrid

Morata Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Morata ya buga wa Chelsea wasanni 47 a gasar firimiya

Dan wasan Chelsea Alvaro Morata ya koma Atletico Madrid a matsayin aro zuwa karshen kakar wasanni 2019/2020.

Morata mai shekara 26, ya je Chelsea ne daga Real Madrid a 2017, kan kudi fam miliyan 60 da yarjejeniyar kwantaragin shekara biyar.

Morata ya buga wa Chelsea wasanni 47 a gasar firimiya ya kuma zura kwallaye sau goma 16 a raga.

Dama dai Morata ya taba buga wa Atletico kwallo lokacin yana karami kafin daga bisani ya sauya sheka zuwa kungiyar Real Madrid.

An duba lafiyar dan wasan a Spain a ranar Lahadi.

Dan kwallon ya koma Atletico Madrid bayan da kungiyarsa ta dauko Gonzalo Higuain a matsayin aro.

Wasan karshe da Alvaro Morata ya yi a Chelsea shi ne wasan da ta yi da Notinam Forest a gasar FA, inda kungiyar ta jefa kwallaye biyu kuma ta hannun Moratan.

Labarai masu alaka