Neymar Junior zai yi jinyar mako 10

Neymar Junior Hakkin mallakar hoto BBC Sport
Image caption Neymar ya fita daga fili ciikin hawaye bayan da ya raunata idon-sawunsa a karawarsu da Strasbourg

Shahararren dan wasan PSG Neymar zai yi jinya har ta tsawon mako goma.

Hakan na nufin dan wasan ba zai samu damar buga duka wasanni biyu na gasar cin kofin Zakarun Turai, inda PSG din za ta kara da Manchester United a watan Fabrariru.

A shekarar 2017 ne Neymar ya koma kungiyar Ligue 1 ta PSG a matsayin dan wasa mafi tsada a duniya a kan kudi fam miliyan 200.

Dan kwallon ya ji raunin ne a wasan gasar French Cup inda PSG ta doke Strasbourg da ci 2-0.

A wata sanarwa kungiyar ta ce: "Ta tara kwararrun masana a fannin lafiya don su duba lafiyar dan wasan."

"Bayan da masanan suka yi nazari, sun cimma matsaya kan yadda za a yi masa magani," in ji PSG.

Har wa yau sun ce dan wasan ya amince da matakin "kuma ana saran zai koma wasa bayan mako 10."

Labarai masu alaka