Dennis Suarez ya koma Arsenal a matsayin aro

Dennis Suarez Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Suarez ya buga wa Barcelona wasanni 71

Kungiyar Arsenal ta karbi aron dan wasan tsakiyar Barcelona Dennis Suarez a kan yarjejeniyar aro.

Yarjejeniyar ta zo ne a jajiberin rufe kasuwar saye da musayar 'yan wasa ta nahiyar Turai.

Dan asalin kasar Spain, Suarez ya buga wa Barcelona wasanni 71 tun bayan komawarsa kungiyar a shekarar 2013, kuma wasanni takwas kawai ya buga mata a kakar bana.

Har ila yau dan wasan ya taka leda a kungiyar Sevilla karkashin kocin Arsenal Unai Emry.

Har yanzu Arsenal na muradin sayen dan wasan tsakiya kuma 'yan wasan Inter Milan Ivan Perisic da Yannick Carrasco mai murza leda a kasar China na cikin wadanda take zawarci.

Duk da cewa Arsenal na fama da 'yan wasa masu rauni, ba a sa ran kungiyar za ta sayi 'yan wasan baya.

Labarai masu alaka