Herrera ya ja kunnen Manchester United

Ander Herera Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ander Herrera ya gargadi 'yan wasan Manchester United da kada su gaza wajen sa kwazo musammam a watan nan da za su buga manyan wasanni.

Herrera mai buga wa United tsakiya ya bukaci 'yan wasa su kara sa kaimi bayan da suka yi nasarar doke Leicester City 1-0 a ranar Lahadi a King Power.

Kocin rikon kwarya, Ole Gunnar Solskjaer ya ci wasa tara da canjaras daya, tun bayan da ya maye gurbin Jose Mourinho wanda United ta sallama a watan Disamba.

Hakan ne ya kai United mataki na biyar a teburin Premier, kuma maki biyu ya rage tsakaninta da Chelsea wadda take ta hudu.

United za ta ziyarci Fulham a gasar Premier a ranar Asabar, sannan ta karbi bakuncin Paris St Germain a gasar cin kofin Zakarun Turai a ranar 12 ga watan Fabrairu.

Daga nan ne United za ta buga gasar kofin FA zagaye na biyar, inda za ta ziyarci Chelsea ranar 18 ga watan Fabrairu, sannan ta karbi bakuncin Liverpool a gasar Premier.

Herrera ya bukaci 'yan wasa su maida hankali wajen karawa da Fulham, kafin su hangi sauran wasannin da za su fafata masu zafi a cikin watan nan na Fabrairu.

Labarai masu alaka