Hazard ya yanke shawara kan makomarsa

Eden Hazard Hakkin mallakar hoto Getty Images

Dan wasan tsakiya na Chelsea, Eden Hazard ya ce ya yanke shawara kan makomarsa a fannin tamaula.

A karshen kakar badi yarjejeniayr Hazard dan kwallon tawagar Belgium za ta kare a Stamford Bridge, bayan da ake alakanta shi da cewar zai koma Real Madrid da taka-leda.

Dan wasan mai shekara 28 ya ce ya yanke shawarar abin da zai yi nan gaba, amma bai fayyace hukuncin da zai dauka ba.

A baya can kocin Chelsea, Maurizio Sarri ya ce ba ya tunanin Hazard zai fayyace makomarsa a Chelsea har sai karshen kakar tamaula ta bana.

Hazard ya koma Chelsea daga Lille a shekarar 2012, ya kuma ci kwallo 15 a kakar shekarar nan.

Labarai masu alaka