Tottenham ta ci gaba da matsa lamba

Tottenham Hakkin mallakar hoto Getty Images

Tottenham ta yi nasarar doke Leicester City da ci 3-1 a wasan mako na 26 a gasar cin kofin Premier da suka fafata a ranar Lahadi a Wembley.

Tottenham ta fara cin kwallo ta hannun Davinson Sanchez a minti na 33 da fara wasa, Leicester ta samu damar farkewa a bugun fenariti, amma Jamier Vardy ya barar.

Bayan da aka koma daga hutu ne Eriksen ya kara na biyu daga baya Vardy na Leicester ya zare daya, sai dai daf da za a tashi daga fafatawar Son Heung-Mi ya ci na uku.

Da wannan sakamakon Tottenham tana nan a mataki na uku da maki 60, maki biyar tsakaninta da Liverpool ta daya a teburi, sannan maki biyu tsakaninta da City wadda za ta karbi bakuncin Chelsea.

A ranar Asabar Liverpool ta doke Bournemouth da ci 3-0 a karawar mako na 26 a gasar ta Premier da suka kara a Anfield.

Labarai masu alaka