Champions League: 'Yan Madrid da za su je Ajax

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images

Real Madrid za ta ziyarci Ajax a wasan farko zagaye na biyu a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League da za su kara a ranar Laraba.

A Champions League takwas da suka buga, Real ta yi nasara a karawa shida, Ajax ta ci wasa biyu.

Sun kuma buga European Cup hudu, inda Ajax ta ci wasa biyu, Real ta yi nasara a daya da kunnen doki a fafatawa daya.

Real Madrid tana da kofin Zakarun Turai na Champions League guda 13, ita kuwa Ajax tana da shi hudu.

'Yan wasan Real Madrid:

  • Masu tsaron raga: Navas da Courtois da kuma Altube.
  • Masu tsaron baya: Carvajal da Vallejo da Ramos da Varane da Nacho da Marcelo da Odriozola da kuma Reguilón.
  • Masu buga tsakiya: Kroos da Modric da Casemiro da Valverde da Asensio da Brahim da kuma Ceballos.
  • Masu cin kwallo: Mariano da Benzema da Bale da Lucas Vázquez da kuma Vinicius Jr.

Labarai masu alaka