Ramos ya buga wa Madrid wasa na 600

Sergio Ramos Hakkin mallakar hoto Getty Images

Sergio Ramos ya buga wa Real karawar ta 600 a wasan da Madrid ta doke 2-1 Ajax gasar Zakarun Turai ta Champions League da suka yi a ranar Laraba.

Real Madrid mai rike da kofin Zakarun Turai kuma 13 jumulla, ta ziyarci Ajax ne a wasan farko zagaye na biyu a gasar ta zakarun Turai.

Ramos kyaftin din Real zai zama saura wasa daya ya kamo yawan wanda Fernando Hiero da Paco Gento suka yi wa Madrid fafatawa.

Mai tsaron bayan, mai shekara 32 zai zama na hudu a jeren wadan da suka buga wa Real wasanni da dama, bayan Manolo Sanchis mai 710 da Iker Casillas mai wasa 725 da kuma Raul Gonzalez mai karawa 741.

Ramos ya koma Real Madrid da murza leda daga Sevilla a shekarar 2005.

A ranar 5 ga watan Maris ne Ajax za ta je Madrid domin buga wasa na biyu.

Labarai masu alaka