PSG ta gano barakar Solskjaer

United PSG Hakkin mallakar hoto Getty Images

Paris St Germain ta yi nasarar cin Manchester United 2-0 a wasan farko zagaye na biyu a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League da suka kara a ranar Talata.

PSG ta fara cin kwallo bayan da aka koma zagaye na biyu a karawar, kuma minti bakwai tsakani Kylian Mbappe ya ci na biyu.

United ta karasa karawar da 'yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Paul Pogba jan kati.

Wannan ne karon farko da kocin rikon kwarya, Ole Gunnar Solsjaer ya yi rashin nasara, tun bayan da ya maye gurbin Jose Mourinho a watan Disamba.

Solskjaer ya ci wasa 10 da yion canjaras daya a fafatawa 11 da ya yi, tun lokacin da aka nada shi kocin rikon kwarya.

Wannan ne karo na biyu da kungiyoyin suka kara a gasar ta cin kofin Zakarun Turai ta Champions League.

Manchester United za ta ziyarci Paris St Germain a wasa na biyu zagaye na biyu a gasar cin kofin Zakarun Turan a ranar 6 ga watan Maris.

Labarai masu alaka