Zan yi murna idan na lashe Europa — Cech

Petr Cech Hakkin mallakar hoto Getty Images

Mai tsaron ragar Arsenal, Pert Cech ya ce zai yi farinciki idan har ya lashe Europa Cup a Arsenal, bayan da ya sanar zai yi ritaya a karshen kakar bana.

A watan Janairu dan wasan mai shekara 36 ya sanar zai hakura da taka-leda da an kammala wasannin 2018/19, bayan da ya ci kofuna 14 a Chelsea da Gunners.

Rashin kokarin Cech a gasar Premier ya sa Bernd Leno ya maye gurbinsa a Emirates, amma shi ne yake tsare ragar Arsenal a wasannin Europa da Caraboa.

Ana sa rana golan shi ne zai tsare ragar Arsenal a wasan da za ta ziyarci BATE Borisov a Europa League a ranar Alhamis, har ya hangi kansa a wasan karshe a gasar.

Labarai masu alaka