Madrid ta doke Ajax a Netherlands

Ajax Real Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kungiyar Ajax ta yi rashin nasara da ci 2-1 a hannun Real Madrid a wasan farko zagaye na biyu a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League da suka fafata a ranar Laraba.

Real ta fara cin kwallo ta hannun Karim Benzema, bayan da aka koma daga hutu, inda Ajax ta farke ta hannun Hakim Ziyech minti 15 tsakani.

Saura minti uku a tashi daga karawar Real Madrid ta kara na biyu ta hannun Marco Asensio.

Ajax ta taka rawar gani a karawar, inda Nicolas Tagliafico ya ci kwallo, amma alkalin wasa ya soke ta, bayan da ya kalli yadda kwallon ya shiga raga a na'urar da ke taimakawa alkalin wasa yanke hukunci.

Real Madrid mai rike da kofin tana da shi 13 jumulla, ita kuwa Ajax tana da guda hudu a tarihi.

Ajax za ta ziyarci Madrid a wasa na biyu a ranar 5 ga watan Maris.

Labarai masu alaka