Champions League: Lyon da Barca

Lyon Barca

Asalin hoton, Getty Images

Lyon za ta karbi bakuncin Barcelona a wasan farko zagaye na biyu a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League da za su fafata a ranar Talata.

Kungiyoyin biyu sun kara a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League sau shida, Barcelona ta yi nasara a wasa hudu suka yi canjaras a karawa biyu.

Barcelona ta lashe kofin Zakarun Turai karo biyar, ita kuwa Lyon ba ta taba dauka ba.

Barcelona tana ta daya a kan teburin La Liga da maki 54, ita kuwa Lyon tana ta uku a kan teburin gasar Faransa da 46.

Tarihin haduwa tsakanin Lyon da Barcelona

2008/2009 CHAMPIONS LEAGUE

11 Maris 2009 Barcelona 5 - 2 Lyon

24 Fabrairu 2009 Lyon 1 - 1 Barcelona

2007/2008 CHAMPIONS LEAGUE

27 Nuwamba 2007 Lyon 2 - 2 Barcelona

19 Satumba 2007 Barcelona 3 - 0 Lyon

2001/2002 CHAMPIONS LEAGUE

23 Oktoba 2001 Lyon 2 - 3 Barcelona

10 Oktoba 2001 Barcelona 2 - 0 Lyon