United ta fitar da Chelsea a FA Cup

Chelsea Man United

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United ta yi nasarar cin Chelsea 2-0 a gasar FA Cup karawar zagaye na biyar da suka fafata a Stamford Bridge a ranar Litinin.

United ta ci kwallon farko ta hanun Ander Herrera minti na 31 da fara tamaula, sannan Paul Pogba ya kara na biyu daf da za a je hutu.

Rabon da United ta yi nasara a Stamford Bridge tun 1-0 da ta doke Chelsea a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions Legue da suka fafata a ranar 6 ga watan Afirilun 2011.

Ko a bara kungiyoyin biyu sun hadu a wasan karshe a gasar cin kofin Kalubalen Ingila, inda Chelsea ta yi nasara da ci 1-0 a ranar 19 ga watan Mayun 2018.

Haka kuma kungiyoyin sun fafata a gasar Premier shekarar nan a Stamford Bridge inda suka tashi 2-2 a cikin watan Oktoban 2018.

United tana da FA Cup 12 da ta lashe jumulla, ita kuwa Chelsea tana da takwas, Arsenal ce mai 13.