Champions League: Shalke da Man City

City Players

Asalin hoton, Getty Images

Manchester City za ta ziyarci Shalke 04 a wasan farko na zagaye na biyu a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League a ranar Laraba.

Kungiyoyin biyu sun kara a gasar zakarun Turai sau uku, inda City ta yi nasara a wasa biyu, Schalke 04 ta ci daya.

Schalke da Manchester City ba su taba daukar kofin Zakarun Turai na Champions League ba.

Manchester City tana ta daya a kan teburin Premier da maki 65, ita kuwa Schalke 04 tana ta 14 a teburin Bundesliga da maki 24.

Ga haduwar da aka yi tsakanin kungiyoyin biyu:

2008/2009 UEFA CUP

27 Nuwamba 2008 Schalke 0 - 2 Man City

1969/1970 EURO CUP WINNERS CUP

  • 15 Afirilu 1970 Man City 5 - 1 Schalke
  • 01Afirilu 1970 Schalke 1 - 0 Man City